Iraqi

ISIS ba ta yi amfani da makami mai guba ba-Iraqi

Iraqi ta wanke ISIS daga zargin amfani da makami mai guba a birnin Mosul
Iraqi ta wanke ISIS daga zargin amfani da makami mai guba a birnin Mosul REUTERS/Suhaib Salem

Jakadan Iraqi a Majalisar Dinkin Duniya, Mohammed Alhakim ya ce, babu wata hujja da ke tabbatar da cewa kungiyar ISIS ta yi amfani da makamai masu guba a yakin da ta gwabza da dakarun gwamnati a birnin Mosul.

Talla

Mr. Alhakim ya ce, ya gabatar da wannan zancen ga Majalisar Dinkin Duniya bayan kammala ganawa da jami’an gwamnatin Iraqi a birnin Bagadaza a jiya Jumma’a.

A farkon watan nan ne, kungiyar bada agaji ta Red Cross ta rawaito cewa, an kwantar da mutane bakwai da suka hada da kananan yara biyar a wani asibitin birnin na Mosul saboda shakar gubar makamin ISIS.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.