MDD

Yunwa za ta kashe mutane da dama-MDD

Kasashen Najeriya da Somalia da Sudan ta Kudu da Yemen na fama da yunwa
Kasashen Najeriya da Somalia da Sudan ta Kudu da Yemen na fama da yunwa Reuters/Feisal Omar

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, a karon farkon tun shekarar 1945, duniya na fuskantar matsalolin rayuwa mafi muni da ke ciwa da jama’a.

Talla

Shugaban hukumar jin-kai ta Majalisar Dinkin Duniya, Stephen O’Brien ya shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar cewa, fiye da mutane miliyan 20 na fama da yunwa ko kuma karancin abinci a kasashen Yemen da Somalia da Sudan ta Kudu da kuma Najeriya.

Mr. Obrien ya ce, ana bukatar agajin Dala biliyan 4.4 nan da watan Juli don tinkarar matsalar.

O’Brien ya kara da cewa, mutane da dama za su rasa rayukansu matukar kasashen duniya suka gaza bada hadin-kai don shawo kan wannan matsalar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.