Iraqi

Birnin Bagadaza na Iraqi ne mafi munin rayuwa a duniya

Iraqi na fama da Rikicin akida da barazanar mayakan IS
Iraqi na fama da Rikicin akida da barazanar mayakan IS REUTERS/Khalid al Mousily

Birnin Vienna da ke kasar Austria ya sake zama birni mafi ingancin rayuwar Bil Adama a duniya, a wani binciken da aka gudanar kan birane 231 na duniya. Birnin Bagadaza ne mafi hatsari a duniya.

Talla

Karo na 8 ke nan a jere da jere da Vienna na zama na daya a duniya a binciken da wani kamfanin Mercer mai zaman kansa ya gudanar.

Binciken ya yi nazari kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya da kula da lafiyar al’umma da ilimi da aikata laifufuka da yanayin siyasa da sufuri.

Manyan birane irin su London da Paris da Tokyo da New York ba su samu damar zuwa kusa da na 30 a binciken ba

Binciken ya bayyana Zurich a matsayi na 2, New Zealand na 3, Munich na 4 sai kuma Vancouver na 5.

Birnin Durban na Afrika ta kudu shi ne na farko a Afrika a matsayin birni mafi ingancin rayuwa a nahiyar amma na 87 a duniya.

Kasashen da ke karshen jerin bnciken sun hada da Damascus na Syria da Bangui na Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Sanaana Yemen da Port-au-Prince na Haiti da Khartoum na Sudan da kuma N’Djamena na Chadi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.