Amurka

Kotunan Amurka na nazari kan dokar Trump

Kotunan Amurka za su yanke hukunci kan dokar hana shigar baki cikin kasar
Kotunan Amurka za su yanke hukunci kan dokar hana shigar baki cikin kasar REUTERS/Noah Berger/File Photo

A yayin da gwamnatin Donald Trump ke shirin fara aiwatar da dokar hana shigar baki cikin Amurka, manyan kotunan tarayyar kasar na zaman nazari kan wannan doka. 

Talla

Wannan na zuwa ne bayan wasu jihohin kasar da kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun shigar da kara kotu don kalubalantar dokar.

Kotunan uku na zaman nazarin ne a Maryland da Hawaii da Seattle na Washington, kuma ana fatan alkalai za su yanke hukunci kan lokaci game da dokar ta hana shigar baki cikin Amurka da shugaba Donald Trump ya farfado da ita.

A ranar 27 ga watan Janairun da ya gabata ne, shugaba Trump ya sanya hannu kan irin wannan doka, yayin da kotunan tarayyar suka yi watsi da ita, amma daga bisani Mr. Trump ya sake kirkiro makamanciyarta don hana ‘yan wasu kasashen Musulmi 6 shiga Amurkan da suka hada da Syria da Yemen da Sudan da Libya da Somalia da kuma Iran.

Gwamnatin Trump dai ta shirya fara aiwatar da dokar ce a gobe, wadda ta bukaci a hana ‘yan gudun hijira shiga Amurka har tsawon kwanaki 120, sannan kuma a dakatar da bada bisa ga ‘yan kasashen na muslmi har tsawon kwanaki 90.

Shugaba Donald da manyan mambobin majalisar ministocinsa da suka hada da Sakataren Harkokin Wajen kasar Rex Tillerson da Alkalin Alkalai, Jeff Sessions da kuma Sakatern Harkokin Tsaron cikin gida John Kelly, duk sun ce, dokar nada muhimmaci wajen hana masu tsattsauran ra’ayi samun shiga Amurka.

Sai dai wasu masharhanta sun ce, dokar wani yunkurin hana Musulmai shiga kasar ne, abin da suka ce ya saba wa kundin tsarin mulkii

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.