Israel-Palestine

Manzon Trump ya gana da Netanyahu da Abbas

Jason Greenblatt, manzon shugaban Amurka Donald Trump ya gana da shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas da firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu domin share fagen shiga tattaunawar farfado da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Palasdinu.

Jason Greeblatt, manzon shugaba Donald Trump
Jason Greeblatt, manzon shugaba Donald Trump Reuters
Talla

Jason Greenblatt, ya gana da Mahmoud Abbas ne bayan ya share tsawon awanni biyar yana tattaunawa da firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu a birnin Quds, kuma jim kadan bayan ganawa da mutanen biyu, manzon na shugaba Trump ya ce ganawar ta yi armashi matuka.

Babbar manufar wannna ziyara da manzon na shugaban Amurka ya kai a Gabas ta Tsakiya ita ce farfado da zaman lafiya, tare da samar da yanayi na yabbatar daa tsaron Isra’ila kamar dai yadda ya bayyana a wani sako a shafin Tweeter.
Wannan dai ita ce ziyarar farko da wani jami’in gwmanatin Donald Trump ya kai a yankin tun daga lokacin da shugaban na Amurka ya karbi ragamar mulki a ranar 20 ga watan janairun da ya gabata.

Kafin wannan ziyara da Jason ya kai a Gabas ta Tsakiya, shugaba Trump ya zanta ta wayar tarho da Mahmoud Abbas a ranar juma’a da ta gabata, inda ma ya gayyace shi zuwa Washington a nan gaba kadan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI