Amurka

Amurka ta dauki alhakin harin da ya kashe mutane a Syria

Mutane fiye da 40 sun mutu a wani harin sama da Amurka ta ce, ita ta kai cikin kuskure
Mutane fiye da 40 sun mutu a wani harin sama da Amurka ta ce, ita ta kai cikin kuskure REUTERS/Anees Mahyoub

Kasar Amurka ta ce ita ta kai wani kazamin harin da ya kashe fararen hula sama da 40 a wani Masallaci da ke Idlib a yankin arewacin Syria.

Talla

Kakakin rundunar sojin kasar, Kanar John J Thomas ya tabbatar da kai harin, amma ya ce ba wai Masallaci suka shirya kai shi ba, sai dai wani ginin sansanin mayakan Al Qaeda.

Jami’in ya ce za su gudanar da bincike kan zargin mutuwar fararen hula.

Shugaban kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam a Syria, Rami Abdel Rahman ya ce, wasu jiragen yaki ne da a fayyace su ba suka kaddamar da farmakin kan masallacin a dai dai lokacin da ake gudanar da sallar magariba.

Rahman ya ce, harin ya fi ritsa wa da fararen hula kuma akwai wadanda baraguzan ginin masallacin suka binne, baya ga sama da 100 da suka jikkata.
 

Rundunar hadaka da Amurka ke jagoranta wajen yaki da mayakan jihadi ta kai hare-haren da suka ritsa da fararen hula a Syria da Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI