MDD

Masu safarar mutane na samun Dala biliyan 150-MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce masu safarar mutane suna bautar da su a kasashen duniya na samun kudin da ya kai Dala biliyan 150 kowacce shekara.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres ya bayyana haka, in da ya ke cewa mutane sama da miliyan 21 aka yi safarar su yanzu haka.

Guterres ya bayyana wannan rahoto mai tada hankali ne wajen taron ministoci kan yadda za’a magance matsalar safarar baki musaman wadanda ke fitowa daga in da ake fama da tashin hankali, da kuma masu tilasta wa jama’a aikin karfi da bautar da mutane.

Sakataren ya ce abin takaici ne yadda aka yi safarar mutane miliyan 21 kamar yadda rahotan kungiyar kwadago ta duniya ya sanar, abin da ya taimaka wa masu hada-hadar samun kudin da ya kai Dala biliyan 150.

Guterres ya ce bayan wannan adadi, akwai kuma dubban mutanen da suka rasa rayukansu wajen tsallakawa da su ta teku da kuma yadda ake cin zarafin mata da 'yan mata a duniya.

Sakataren ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda ake tilasta wa 'yan mata aikin karuwanci da auran dole.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI