Amurka

Gwamnatin Trump ta daukaka kara kan dokar baki

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump 路透社

Gwamnatin Donald Trump ta daukaka kara don kalubalantar hukuncin da wata Kotun Maryland ta dauka na dakatar da dokar hana shigar baki daga kasashen Musulmi shida cikin Amurka.

Talla

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu da Kotun ta Maryland da kuma ta Hawaii suka yanke hukuncin cewa, dokar wani yunkurin nuna wariya ne ga Musulmin.

Shugaba Donald Trump dai ya ce akwai bukatar kafa wannan doka don kare Amurka daga barazara tsaro da kuma masu tsattsauran ra’ayi, abin da ya sa gwamnatinsa ta daukaka kara a kotun Richmond da ke Virginia.

Kasashen Musulmin da dokar ta shafa sun hada da Somalia da Sudan da Yemen da Libya da Syria da Iran.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI