Amurka-Jamus

NATO na bin Jamus bashin Makudan kudade-Trump

Shugaba Donald Trump a lokacin ganawarsa da Angela Merkel ta Jamus
Shugaba Donald Trump a lokacin ganawarsa da Angela Merkel ta Jamus REUTERS/Jim Bourg

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce kungiyar NATO na bin Jamus bashin Makudan kudadde, tare da bukatar Berlin ta rubanyawa Washington kudadden tsaro.

Talla

Kallaman Trump na zuwa kwana guda bayan ganawarsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

A ganawar da suka yi jiya Juma’a a birnin Washington da Merkel ta kai ziyarar, shugabanni sun nuna yiwuwar daidatawa da kuma batun Kungiyar NATO da kudadde da ake kashewa Tsaro.

Sai dai a yau Assabar Mista Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa NATO na bin Jamus dimbin bashi kuma dole a biya Amurka sosai kafin ta bai wa kasar tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.