Faransa

Yarima William na Birtaniya na ziyara a Faransa

Yarima William da matarsa Kate
Yarima William da matarsa Kate REUTERS/Phil Noble

Yarima William na Birtaniya ya yi alkawarin cewa, kasarsa za ta ci gaba da hulda da Faransa bayan ficewarta daga Kungiyar Taraayyar Turai.

Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da Yarima William da matarsa Kate ke ziyarar kwanaki biyu a birnin Paris.

A karon farko kenan da William ke kai ziyara Faransa a hukumance tun bayan mutuwar mahaifiyarsa Diana a wani hatsarin mota da ya ritsa da ita a shekara ta 1997 a Paris.

Tuni dai William da matarsa suka gana da shugaban Faransa Francois Hollande, sannan kuma a yau Asabar ne za su gana da wadanda harin ta’addancin ISIS ya shafa shekaru biyu da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI