Amurka

Za mu dauki matakin soji kan Koriya ta Arewa- Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson a birnin Seoul na Koriya ta Kudu
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson a birnin Seoul na Koriya ta Kudu Reuters/路透社

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson zai jaddada sabon kudirin kasarsa kan Koriya ta Arewa a tattaunawar da zai yi da mahukuntan China a wannan Asabar. 

Talla

Gwamnatin Donald Trump ta yi amfani da ziyarar da Tillerson ke yi a kasashen Asia wajen bayyana matakinta na kawo karshen lalama da Koriya ta Arewa da ta yi gwaje-gwajen makamai masu linzami.

Mr. Tillerson ya ce, Amurka a shirye take da dauki matakin soji kan Koriya ta Arewa matukar ta ci gaba da yin barazana ta hanyar gwajin makamin Nukiliya.
 

Amurka na da kimanin dakaru dubu 28 da ta girke a Koriya ta Kudu don kare ta daga barazanar Koriya ta Arewa.

Amma birnin Seoul na tsakan-kanin zangon da makamin Koriya ta Arewa zai iya cimma, yayin da masharhanta suka yi amanna cewa, duk wani rikici tsakanin bangarorin biyu zai haddasa asarar rayuka da dama.

Sai dai wannan fargabar ba ta hana Amurka fadin cewa, ta kawo karshen lalama da Koriya ta Arewan ba, kamar yadda gwamnatin Barrack Obama ta dauka a can baya.

Koriya ta Arewa dai na da dadaddiyar burin zama kasa mai karfin makamin Nukiliya a duniya, in da ta ce tana bukatar kare kanta daga duk wata barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.