Amurka

James Comey da Rogers za su bayyana a gaban Majalisa kan Rasha

FBI zata bayyana gaban Majalissa kan Rasha
FBI zata bayyana gaban Majalissa kan Rasha Reuters/Joshua Roberts

A wannan litinin shugaban hukumar FBI James Comey da takwaransa na hukumar tsaron cikin gida Admiral Mike Rogers za su bayyana a gaban kwamitin majalisar kasar da ke binciken zargin da Amurka ke yi wa Rasha na yin shisshigi a lokacin zaben shugabancin kasar da ya gabata.

Talla

Kwana daya kafin wadannan mutane sun gurfana a gabansu, shugaban kwamitin bincike dangane da bayanan sirri a Majalisar Wakilan kasar Devin Nunes, ya ce kawo yanzu ba wasu hujojin da ke tabbatar da cewa akwai wata alaka tsakanin yakin neman zaben Donald Trump da kuma kasar Rasha.

Dan majalisar wakilai Devin Nunes, wanda ke zantawa da tashar talabijin ta Fox News ya bayyana haka ne kwana daya kafin shugaban hukumar bincike ta FBI James Comey ya gurfana a gaban kwamitin da ke binciken wannan zargi da tsohuwar gwamnatin Amurka ke yi wa Rasha.

Nunes, wanda jam’iyyarsu daya da Donald Trump wato Republican, ya zargi wasu daga cikin manyan jami’ai a hukumomin tara bayanan sirrin kasar ta Amurka da fallasa wasu bayanan domin kawo cikas ga mulkin Trump, inda ya ce tabbas, ‘’wannan ita ce babbar manufarsu’’.

A cikin watan jiya ne aka fallasa bayanan da ke cewa wanda Trump ya nada domin ba shi shawara kan sha’anin tsaro Michael Flynn, ya taba ganawa da jakadan Rasha a Amurka kafin bikin rantsar da shugaban cikin watan janairun da ya gabata, lamarin da ya tilasta ma sa yin marabus daga mukaminsa.

Har yanzu dai akwai ‘yan jam’iyyar Democrat da dama da ke zargin cewa Rasha ta yi kutse a shafin yanar gizo na yakin neman zaben Hillary Clinton, lamarin da ya yi matukar taimaka wa Donald Trump domin yin nasara a wannan zabe, zargin da kwamitin da Devin Nunes ke ci gaba da bincike domin tabbatar da gaskiyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI