Mexico

Mexico ta yi barazanar dakatar da sayen Masarar Amurka

Mexico na sayen Masarar Amurka domin ciyar da dabbobinta
Mexico na sayen Masarar Amurka domin ciyar da dabbobinta REUTERS/Kim Kyung-Hoon/File Photo

Kasar Mexico ta yi barazanr dakatar da sayen masara daga kasar Amurka sakamakon takaddamar da ta barke tsakanin kasashen biyu tun bayan rantsar da shugaba Donald Trump.

Talla

Matakin dai barazana ne ga manoman Amurka da ke Jihohin Iowa da North Dakota da Kansas da Missouri da kuma Nebraska domin Mexico ce ke saye daukacin Masarar da suke nomawa.

Thomas Sleight, shugaban kungiyar masu noman masara a Amurka ya ce lallai hankalin su ya tashi domin Mexico ce kasa ta farko da ke saye amfanin gonarsu.

Yanzu dai haka ministan noman Mexico na tattaunawa da kasashen Brazil da Argentina domin ganin yadda za su karkata akalar cinikayyarsu daga Amurka.

Sai dai kuma Masarar Amurka ta fi sauki akan Masarar da ake nomawa a Brazil da Argentina.

Matakin Mexico na zuwa bayan Trump ya yi barazanar rusa yarjejeniyar kasuwancin bai-daya ta NAFTA tsakanin Amurka da Mexico da Canada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.