Za a yi matsanancin Zafi a 2017
Wallafawa ranar:
Binciken Majalisa Dinkin Duniya ya nuna cewar a bana za a fuskanci matsanancin zafin kamar na bara da aka bayyana mafi tsanani da aka taba fuskanta a duniya.
David Carlson, shugaban hukumar binciken yanayi ta Majalisar ya ce ko da babu matsalar fari da aka yi wa lakabi da El Nino wanda ta haifar da matsalar tsakanin shekaru 4 zuwa 5 da suka gabata, shekarar 2017 na tafe da wasu sauye sauye da ke kalubalantar sanin da suka yi wa yanayin.
An dai wallafa wannan gargadi ne ranar talata a rahotan hukumar na shekara shekara, wanda ya tabbatar da cewar shekarar 2016 ita ce mafi zafi a tarihi.
Ma’aunin zafin ya kai 1.1 na Celsius fiye da na bara 0.06.
Rahoton ya ce gurbataccen iskan da ake fitarwa musamman a kasashe masu manyan masana’antu ne ke haifar da dumamar yanayin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu