Argentina

Argentina ta bude kofa ga ‘Yan gudun hijirar Syria

Syria na cikin kasashen da Trump ya haramtawa shiga Amurka
Syria na cikin kasashen da Trump ya haramtawa shiga Amurka REUTERS/Kai Pfaffenbach

Gwamnan Lardin San Luis a kasar Argentina, George S. ya bude kofa ga ‘yan gudun hijirar da suka fito daga kasar Syria. Kuma an kaddamar da wani shiri na biya wa ‘yan gudun hijirar kudin jirgi daga Syria domin isa kasar Argentina.

Talla

Lardin na San Luis ya fara karbar ‘yan gudun hijirar Syria 10.

Gwamnatin lardin San Luis, ta ce za ta ware makudan kudade don samar da kulawar lafiya kyauta ga ‘yan gudun hijirar na Syria da gina musu matsuguni da kuma samar mu su da ayyukan yi.

Sanarwar na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump, ya sanya hannu kan dokar hana bakida ‘yan gudun hijira shiga kasar daga kasashen Muslmi 6 cikin har da Syria. Dokar da har yansu Trump ke fafatawa da kotunan Amurka don tabbatar da ita.

Daga shekara ta 2014 kawo yanzu gwamnatin kasar Argentina da hadin gwiwar lardunanta musamman na San Luis ta karbi sama da ‘yan gudun hijirar kasar Syria 1, 600. Sai dai duk da kokarin kyautatawa ‘yan gudun hijirar gwamnatin kasar ke yi, akan samu rahotanni jefi jefi na yadda wasu ‘yan Argentina da ke nuna musu wariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.