Amurka

Kasashe 68 sun lashi takobin murkushe ISIS

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, yayin taron kasashe 68 da ya gudana a birnin Washington.
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, yayin taron kasashe 68 da ya gudana a birnin Washington. REUTERS/Joshua Roberts

Manyan jami’an diflomasiyya na kasashen duniya 68, sun lashi takobin gaggauta kawo karshen ayyukan kungiyar IS.

Talla

A taron da suka gudanar a birnin Washington, wakilan kasashen da ke cikin kawancen fada da wannan kungiya a karkashin jagorancin Amurka, sun ce nan ba da jimawa ba zasu kawo karshen shugaban kungiyar ta IS.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, wanda ke gabatar da jawabi a wurin taron, ya ce babban abin da suka sanya a gaba shi ne gaggauta gano inda shugaban kungiyar ta IS Abubakar al-Baghdadi ya boye.

Tillerson ya ce an kashe illahirn mataimakan al-Baghadadi a Iraki da Syria, cikinsu har da wadanda suka kai hare-hare a kasahen ketare da suka hada Beligium da kuma Faransa, kuma nan ba da jimawa ba za’a ga bayan wanda ke kiran kansa Khalifa.

Taron dai na a matsayin dama ga Amurka domin bayyana wa kasashen irin shirin da gwamnatin Donald Trump ta yi, domin fada da ayyukan wannan kungiya, wadda yanzu haka take ci gaba da iko da wasu yankuna a kasashen Iraki da Syria.

Tun a shekara ta 2014 ne tsohuwar gwamnatin Barack Obama, ta kafa rundunar tare da sauran kasashen duniya domin yaki da kungiyar ta IS, wadda ta yi amfani da rikicin cikin gida a kasashen Syria da Iraki domin mamaye yankuna, da kuma kasancewa babbar matattara ta ‘yan ta’adda a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI