Sufuri

Matakin bai daya kan hana daukar komfuta a jiragen sama ya dace - ICAO

Wani jami'in bincike da ke tantance fasinja a filin jiragen sama na San Francisco da ke birnin California, kasar Amurka.
Wani jami'in bincike da ke tantance fasinja a filin jiragen sama na San Francisco da ke birnin California, kasar Amurka. REUTERS/Robert Galbraith

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta duniya ICAO, ta ce kowacce kasa na da hurumin daukar irin matakan kasashen Amurka da Birtaniya, na hana tafiya da na’urar komfuta da sauran na’urorin lantarki, a jiragen saman fasinja.

Talla

Hukumar wadda tace tana bukatar daukar matakin bai daya, na hana shiga da konfuta jiragen fasinja, ta kara da cewa kasashe ne ke da hurumin aiwatar da dokar ko kuma bijire mata.

Zalika ICAO, ta bayyana matsayin ta ne bayan matakin da Amurka da Birtaniya suka dauka, kuma yanzu haka Faransa da Canada sun ce suma suna nazari akai.

A shekara ta 2016 hukumar kula da sufurin jiragen saman, ta haramta daukar batira masu dauke da sinadarin Lithium a jiragen sama fasinja, har sai masana sun kammala bincike, don fito da sabbin madaukan da suka dace da za’a iya amfani da su wajen daukar batiran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.