Amurka

Ci gaba ko kuma soke shirin kiwon lafiya na ObamaCare

Wasu daga cikin masu zanga zangar adawa da dokar Donald Trump
Wasu daga cikin masu zanga zangar adawa da dokar Donald Trump REUTERS/Aaron P. Bernstein

A yau juma'a majalisar wakilan kasar Amruka ke jefa kuri’ar amincewa  ko ci gaba da tsarin inshorar kiyon lafiya da tsohon shugaban kasar Barack Obama ya samar wa sama da al’ummar kasar milyan 40 shekaru 7 da suka gabata.

Talla

Dama dai tun a lokacin yakin neman zabensa shugaban kasar Donald Trump, ya dau alkawalin soke shirin da zarar ya dare mulki, sakamakon sabanin ra’ayin siyasa dake tsakaninsa da tsohon shugaban Barrack Obama.
Ana ci gaba da dakon sakamakon zaben duk da cewa wasu yan siyasa sun bayyana damuwa a kai, da cewa soke shirin zai iya kawo koma baya ta fuskar kiwon lafiya a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI