Syria-Amurka

Kasashen kawance na cikin shiri domin kawo karshen kungiyar IS

Dakarun Gwamnatin kasar Syria zuwa Raqa
Dakarun Gwamnatin kasar Syria zuwa Raqa REUTERS/Rodi Said/File Photo

Kasashen kawance da ke yakar mayakan IS za su kaddamar da farmakin karshe na kakkabe mayakan daga cibiyarsu da ke Raqa a Syria sanarwa daga rundunar sojin kasashen .

Talla

Ministan tsaron faransa Jean-Yves Le Drian dake tabbatar da wannan yunkuri, ya ce farmakin zai kasance mafi girma da za a kaiwa IS don gani an kawo karshan su a Syria, kamar yadda ake fafatawa da su a Mosul na Iraqi.

IS na fuskantar farmaki daga bangarori da dama a arewacin Syria, inda Rasha ke bai wa dakarun Shugaba Assad cikakken goyon baya, a bangare guda kuma Turkiya na taimakawa kungiyoyin ‘yan tawaye dake yakar Mayakan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.