Majalisar Amurka ta dage kuri'ar rusa Obamacare
Wallafawa ranar:
Majalisar Wakilan Amurka ta dage kada kuri’ar rusa shirin inshoran lafiyar kasar da ake kira Obamacare saboda rarrabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan Jam’iyyar Republican.
Shugaba Donald Trump dai ya sha alwashin soke shirin, amma 'yan Majalisun na bayyana damuwa saboda ganin babu wani shiri da aka gabatar wanda zai maye gurbin Obamacare.
Tsohon shugaban kasar Barack Obama ya yi kira ga 'yan Majalisun da su kauce wa soke shirin wanda yanzu haka ke taimaka wa Amurkawa sama da miliyan 20.
Wannan dai ba karamin koma baya ba ne ga shugaba Trump wanda ya bukaci kada kuri’ar a yau juma’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu