Benin- Faransa

Benin na bukatar Faransa ta maido mata da kayan tarihi

Shugaban kasar Benin Patrice Talon
Shugaban kasar Benin Patrice Talon rfi

Kasar Benin dake yammacin Africa ta nemi kasar Faransa da ta maido mata da wasu kayayyaki na tarihi da aka kwashen a lokacin mulkin turawan  Faransa.

Talla

‘Yan Majalisar Dokokin kasar ta Benin tare da kungiyoyin fararen hula sun rubutawa Shugaban Faransa Francois Hollande wasika domin ganin an maidowa kasar da dukkan kayayyakin tarihi da aka yi gaba dasu.

Ire-iren wadannan kayayyakin tarihi dai yanzu haka suna gidan tarihi na Faransa an yi ado da su.

Faransa ce ta mulki kasar Benin har zuwa shekara ta 1960, a lokaci da ake kiran Benin kasar Dahomey.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.