China- Brazil

Kasar China ta maido da tsarin sayen nama daga Brazil.

Shugaba Michel Temer na kasar Brazil
Shugaba Michel Temer na kasar Brazil REUTERS/Adriano Machado

Hukumomi a kasar Brazil sun sanar da dage haramcin kai nama kasar China bayan da aka sami takaddama da ta kai ga daina cinikin tsakanin kasashen biyu na tsawon wani lokaci.

Talla

Ministan Ayyukan gona na Brazil Blairo Maggi ya sanar da maido da safarar nama daga Brazil zuwa China a cikin wata sanarwa da ya bayar.

Yana mai cewa kasar China ta amince yanzu a kai mata nama daga kasar Brazil.

 

Nama ya kasance abu na uku cikin manyan abin arziki da Brazil ke samun kudaden shiga daga kasashen waje.

Ranar 20 da watannan ne dai kasar China ta haramta kai naman kasar Brazil cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.