Amurka

An kai hari gidan rawa a Ohio na kasar Amurka, mutun daya ya mutu

Rahotanni daga kasar Amurka na cewa mutun daya ya rasa ransa wasu 15 kuma na can da raunuka sakamakon hare-harben bindiga da aka kai  wani gidan rawa a garin Cincinnati dake jihar Ohio.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. rfi
Talla

Majiyoyin ‘yan sanda na cewa da fari an zaci ‘yan bindiga biyu ne suka yi ta bude wutan amma kuma wani jami’in ‘yan Sanda na yankin Paul Neudigate ya sanar da cewa mutun daya ne yayi ta bude wuta amma kuma suna ci gaba da gudanar da bincike sosai.

Ya bayyana cewa babu masaniya ko harin ta’addanci ne aka kai gidan rawan.

A cewar Jami'in 'Yan Sandan wannan  gidan rawa na cike makil da jama’a a lokacin da aka kai harin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI