Masar

Kotun Masar ta daure mutane 56 saboda sakacin mutuwar bakin haure 202 a teku.

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sissi
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sissi REUTERS/Carlo Allegri

Wata kotu a kasar Masar yau lahadi ta zartar da hukuncin dauri na tsawon shekaru tsakanin bakwai zuwa goma kan wasu mutane 56 da ake zargi da hannu wajen sakaci da ya kai ga mutuwar mutane 202 bakin haure a teku.

Talla

25 daga cikin mutanen a bayan idanunsu aka zartar masu da hukuncin daurin, yayinda mutane 31 a kan idanunsu aka bayyana masu hukuncin kotun.

A ranar 21 ga watan Satumba na shekarar data gabata ne wani jirgin ruwa da aka kera shi da katako mallakin mutanen da aka zartas masu da daurin, ya dibi bakin haure don tafiya kasar Italiya,akan hanyarsu ta zura Turai inda a can tsakiyar teku jirgin ya nutse da mutanen.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.