WHO

An bukaci rage farashin maganin warkar da cutar hanta

Likitoci da Na'urorin gwajin cutar Hanta ta hepatitis B
Likitoci da Na'urorin gwajin cutar Hanta ta hepatitis B REUTERS/Baz Ratner

Wasu kungiyoyin kula da lafiya na duniya na kalubalantar tsadar farashin maganin cutar hanta da wani kamfanin samar da magani na Amurka ya samar domin magance cutar da ke barazana ga rayukan miliyoyin mutane.

Talla

Kungiyoyi sa-kai sama da 30 daga kasashen Turai ne suka bukaci kamfanin ya rage farashin maganin da aka tabbatar zai warkar da kashi 90 na cutar hanta ta hepatitis C.

Samar da maganin da ake kira Sofos-buvir ya wanzar da farin ciki ga miliyoyin mutanen da ke fama da cutar ta hanta da ake kira hepatitis C a turance.

Amma kungiyoyin kula da lafiya na duniya na kuka da tsadar maganin inda ake sayar da kwaya guda kacal akan kusan euro dubu daya a Faransa.

Kuma majinyaci zai kashe kudi da ya kai sama da euro dubu 41 a makwanni 12 yana shan maganin.

Yanzu haka kungiyoyin lafiya 30 daga kasashen turai 17 da suka kunshi kungiyar likitoicn duniya ta MDM da kuma ta MSf sun bukaci rage farashin bayan sun shigar da kara a Munich.

Kungiyoyin na son a samar da wani irin sa da ba zai fi karfin masu dauke da cutar ba.

Majalisar Dinkin Duniya  tace mutane kusan miliyan 150 ke dauke da cutar a fadin duniya, kuma hukumar lafiya ta duniya tace kusan mutane dubu dari bakwai ke mutuwa duk shekara sakamakon cututtukan da suka shafi anta a duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.