Duniya

Kasuwar Mai a Duniya

kungiyar OPEC ta masu arzikin mai a Duniya
kungiyar OPEC ta masu arzikin mai a Duniya

Kasashen dake kungiyar OPEC ta masu arzikin mai da wadanda basa ciki sun bayyana shirin kara wa’adin rage yawan man da suke hakowa domin daga farashin sa a kasuwannin duniya. 

Talla

Kwamitin ministocin man ya bayyana gamsuwar sa da yadda kasashen ke aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla na rage yawan man da kowacce kasa ke hakowa, sun bayyana ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar na Karin watanni shida masu zuwa.

Taron ministocin kasashen a Kuwait ya bukaci wani kwamiti ya yi nazari kan kara rage man dan yiwa taron su bayani a wata mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI