Amurka

Shugaba Donald Trump ya dau alkawalin kawo sabon shiri

Donald Trump Shugaban  Amurka
Donald Trump Shugaban Amurka REUTERS/Carlos Barria

Bayan Gazawar sa wajen soke shirin inshoran lafiya da ake kira Obamacare, shugaban Amurka Donald trump ya yi alkawarin kawo wani sabon shirin da zai maye gurbin shirin inshoran wanda yace wannan ba mai dorewa bane.

Talla

Trump ya ce shirin Obamacare zai rushe saboda haka zai kawo wani shiri na dabam, bayan ya zargi ‘yan Jam’iyyar sa ta Republican da rashin samun nasara a zauren Majalisa.
Amurkawa da dama ne suka nuna adawa kan bukatar Shugaba Trump da  cewa , kokarinsa na rusa wannan shiri sai mayar da hannun agogo baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.