Libya

Bakin haure 146 sun bace a teku

Bakin haure 146 sun bace a tekun Mediterranean
Bakin haure 146 sun bace a tekun Mediterranean REUTERS/Dimitris Michalakis

Hukumar Kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, kimanin bakin haure146 sun bace bayan kwale-kwalensu ya kife da su a tekun Mediterranean jim kadan da barin Libya.

Talla

Wani dan asalin kasar Gambia da aka ceto daga hatsarin ya ce, akwai kananan yara da mata masu juna biyu da ke cikin kwale-kwalen.

Mutumin wanda ke kwance a wani asibisti da ke tsibirin Lampedusa a Italiya ya ce, Fasinjojin sun hada da ‘yan Najeriya da Mali da Gambia.

Hukumar kula da kaura ta duniya ta ce, akalla ‘yan gudun hijira 590 ne suka rasa rayukansu ko kuma suka bace a gabar tekun Libya a cikin wannan shekarar.

Hukumomin Italiya sun ce, sun ce sun yi wa ‘yan gudun hijira dubu 23 rajista a cikin wannan shekarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI