China-Faransa

China ta bukaci a kare 'yan kasarta a Faransa

Shugaba Xi Jinping na China
Shugaba Xi Jinping na China 路透社

China ta bukaci Faransa da ta kare lafiyar 'yan kasar ta da ke zama Paris bayan da 'Yan Sanda suka kashe wani dan kasar.

Talla

Wannan ya sa mutanen kasar China suka gudanar da zanga zangar nuna bacin ran su da kisan, kuma 'Yan Sanda suka kama mutane 35 daga cikin su.

Rahotanni sun ce wasu ne suka tseguntawa jami’an 'Yan Sandan cewar ana tashin hankali a gidan mutumin inda suka sheka zuwa gidan, inda akace mutumin ya kai hari kan daya daga cikin jami’an 'Yan Sanda su kuma suka harbe shi.

Sai dai iyalan mutumin sun ce ba haka lamarin ya ke ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI