Birtaniya-EU

Martanin kasashen duniya kan ficewar Birtaniya

Wasikar ficewa da  Birtaniya ta mika wa mahukuntan kungiyar kasashen Turai
Wasikar ficewa da Birtaniya ta mika wa mahukuntan kungiyar kasashen Turai REUTERS/Yves Herman/Photo illustration

Shugabannin kasashen duniya sun mayar da martani bayan Birtaniya ta mika wasikar ficewarta daga kungiyar kasashen Turai don kawo karshen zamanta na shekaru 44 a cikin EU.

Talla

Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump ta bayyana fatanta na ganin cewa, Birtaniya ta ci gaba da kasancewa jigo a yankin Turai duk da cewa ta fara janyewa daga EU.

Mai Magana da yawun fadar White House Sean Spicer ya ce, suna mutunta zabin al’ummar Birtaniya da suka kada kuri’ar ficewa watanni tara da suka shude.

Mambobin Majalisar Dokokin kasashen Turai sun jaddada cewa, babu wata tattaunawa da za su yi game da makomar huldarsu da Birtaniya har sai an kammala cika sharuddan ficewar baki daya.

Shugaban Tarayyar Turai, Donald Tusk ya bayyana wannan rana a matsayin ta bakin ciki, yayin da ya ce, sun yi kewar Birtaniya.

Shugaban Faransa Francois Holland cewa ya yi, ficewar Birtaniya na da sosa rai ga Turai, amma hakan zai yi ma ta illa ta fannin tattalin arziki.

Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus Uwargida Angela Merkel cewa ta yi, lallai kasarta da sauran mambobin EU 27 ba sa son ganin wannan rana ta ficewar saboda za su rasa wata mamba mai muhimmanci a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.