Israel-Palestine

Isra'ila ta bada umarnin gine-gine a yankin Falasdinawa

Kasashen duniya sun caccaki Isra'ila game da karya dokokin kasa-kasa da suka haramta gine-ginen da suka saba ka'ida
Kasashen duniya sun caccaki Isra'ila game da karya dokokin kasa-kasa da suka haramta gine-ginen da suka saba ka'ida AHMAD GHARABLI / AFP

Gwamnatin Isra’aila ta bada umarnin gina sabbin rukunan farko na gidajen Yahudawa a gabar Yamma ga Kogin Jordan da ta mamaye fiye da shekaru 20 da suka gabata, lamarin da ya gamu da suka daga kasashen duniya.

Talla

Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar a jiya Alhamis ta ce, za a yi ginin ne a yankin Emek Shilo da ke kusa da Nablus a gabar Kogin na Jordan.

Matakin dai na zuwa ne kasa da mako guda da Majalisar Dinkin Duniya ta caccaki Isra’ila saboda rashin daukan matakan dakatar da gine-ginenta a yankin Falasdinawa kamar yadda kwamitin tsaro ya bukata a cikin watan Disamban bara.

Kazalika Isra’aila ta dauki matakin ne a rana guda da dubban al’ummar Falasdinu ke tunawa da ranar da jami’an tsaron Isra’ila suka kashe Falasdinawa shida da ke zang-zangar lumana a shekarar 1976 .

Tuni dai hukumomin Falasdinu suka caccaki matakin na Netanyahu da suke kallo a matsyin yunkurin kara dakula shirin samar da zaman lafiya tsakanin bangarotrin biyu.

Wani mamba a kwaitin zartarwar kungiyar fafutukar tabbatar da ‘yancin Falasdinawa Hana Ashrawi ya ce, matakin da Isra’ila ta dauka ya nuna cewa, ta fi mayar da hankali wajen kyautata wa Yahudawa ‘yan share wui zaune fiye da tabbatar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Dokokin kasashen duniya dai na kallon mamayar Isra’ila a matsayin abin da ya sabawa ka’ida, amma kasar ta musanta haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.