India-Najeriya

An kama masu kai wa daliban Najeriya hari a India

An kama masu kai wa daliban Afrika da suka hada da 'yan Najeriya hari a India
An kama masu kai wa daliban Afrika da suka hada da 'yan Najeriya hari a India REUTERS/Shailesh Andrade

Jami’an ‘yan sandan India sun cafke mutane shida da ake zargi da hannu wajen kaddamar da farmaki kan daliban Najeriya da ke karatu a kasar, abin da masu rajin kare hakkin dan adam suka bayyana a matsayin laifin nuna kyama.

Talla

Wasu hotuna da aka watsa a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wasu matasan India ke amfani da sandina da kujerun karfe wajen dukan daliban Najeriya a Greater Noida.

Wani babban Jami’an ‘yan sandan kasar Sujata Singh ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, nan gaba za su sake kama wasu mutane hudu da ake zargi a wannan lamari da ya dauki hankulan ‘yan Najeriya.

Hukumomin Najeriya sun kira jakadan India a kasar don amsa tambayoyi a birnin Abuja kan wannan batu.

An dai kai wa ‘yan Najeriyar hari ne bayan mutuwar wani dan India sakamakon kwan-kwadon kwayoyi fiye da kima, amma mazauna yankin Greater Nida suka zargi ‘yan Najeriya da hannu a mutuwarsa.

Kazalika farmakin ya shafi sauran daliban nahiyar Afrika da ke karatu a kasar ta India, lamarin da ya sa jami’an tsaro ke yi musu rakiya zuwa makarantu da shaguna don kare lafiyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.