Shirin tambaya da Amsa ya duba tarihin Kocin Chelsea Antonio Conte kamar yadda masu saurare suka bukata, Kana mun amsa tambaya kan ciwon Mantuwa da bayani kan makami mai guba. A yi sauraro lafiya tare da Umaymah Sani Abdulmumin.
Sauran kashi-kashi
-
Tambaya da Amsa Tarihin sarkin Lafiyar Baribari na jihar Nasarawa Alh. Sidi Bage Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan mako tare da Micheal Kuduson ya kawo muku wasu daga cikin tambayoyi da wasu masu sauraron mu suka nemi karin bayani, ciki harda tarihin sarkin Lafiyar Baribari dake jihar Nasarawa a Najeriya, Alhaji Sidi Bage Mohammed. Sai kuma batun matsalar tattalin arzikin kasar Ghana.03/06/2023 19:59
-
Tambaya da Amsa Yaya hukumar kididdiga ta kasa ke aikin tattara bayanan farashin kayayyaki Kamar yadda aka saba, shirin 'Tambaya Da Amsa' tare da Michael Kuduson na zuwa muku ne duk mako da amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana. Daga cikin taambayoyin da aka amsa a shirin wannan makon, har da karin bayani kan yadda hukumar kididdiga ke aikinta masamman na tattara farashi.27/05/2023 19:59
-
Tambaya da Amsa Bayani akan sanya wa na’ura basiran dan’adam wato “Artificial Intelligence” Kamar yadda aka saba, shirin Tambaya Da Amsa na zuwa muku ne duk mako da amsoshi daidai gwargwado iko na tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman karin bayani a kan fasahar sanya wa na’ura basirar dan’adam wato “Artificial Intelligence”.20/05/2023 19:58
-
Tambaya da Amsa Takaitaccen tarihin wasan Hotungo na gargajiyar Fulani a Nijar Kamar yadda aka saba, shirin 'Tambaya Da Amsa' yana zuwa muku ne duk mako da amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana. Daga cikin taambayoyin da aka amsa a shirin wannan makon, akwai wadda ke neman talkaiccen tarihin wasan Hotungo da Fulani ke yi a Jamhuriyar Nijar, da kuma tambayar da ta nemi sanin mahimmancin bada takardar shaidar aure a Musulunci.13/05/2023 19:59
-
Tambaya da Amsa Menene musabbabin rikicin Sudan? Shiri 'Tambaya Da Amsa' yana kawo muku amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu sauranmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa muku a wannan tasha, kuma lokaci iri wannan. A cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin musababbin yakin da ake yi a Sudan yanzu haka. Wannan tambayar ma wasu ne za ku ji amsoshinsu a cikin wannan shirn.06/05/2023 20:00