Italiya

G7 : An bukaci Rasha ta yanke hulda da Assad

Taron Ministocin harakokin wajen kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya
Taron Ministocin harakokin wajen kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya REUTERS

Batun huldar Rasha da Syria na cikin manyan batutuwan da suka mamaye taron Ministocin harakokin wajen manyan kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya da ake kira G7 wanda ake gudanarwa a Italiya.

Talla

Kasashen 7 da suka hada da Amurka da Birtaniya da Faransa da Canada da Jamus da Italiya da kuma Japan ana sa ran za su bukaci Rasha ta Janye goyon bayan da ta ke wa shugaban Syria Bashar al Asad musamman bayan harin da aka kai da makami mai guba.

Taron na kwanaki biyu ne da ake gudanarwa a garin Tuscan na Lucca a kasar Italiya.

Amurka ce ta fara matsin lamba ga Rasha akan ta katse hulda da shugaban Syria Bashar Al Assad musamman bayan hari mai guba da aka kai yankin da yan tawayen Syria ke iko wanda ya kashe akalla mutane 87.

Batun harin mai guba kuma na cikin manyan batutuwan da suka mamaye taron ministcoin kasashen na G7.

Amurka ta gargadi Rasha cewa dangantakarsu za ta kara tsami idan har aka sake kai wani hari mai guba, kuma ba za ta taba amincewa da wani matakin sasantawa ba muddin Assad na kan karagar mulki.

A gobe ne ake sa ran sakateren harakokin wajen Amurka Rex Tillerson zai gana da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov kan batun Syria. Yayin da kuma taron ministocin G7 zai tattauna tare da daukar mataki na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.