Syria

An Kashe Fararen Hula 39 a Syria

Jerin dogayen motoci da aka kaiwa hari a Syria
Jerin dogayen motoci da aka kaiwa hari a Syria REUTERS/Ammar Abdullah

A kasar Syria an kai wani kazamin harin Bam kan ayarin fararen hula da ake jigilansu daga kauyukan ‘yan Shia da dogayen motoci karkashin wani tsarin kaisu tudun mun tsira.

Talla

Mutane 39 suka mutu nan take tare da lalata dogayen motocin.

Wannan hari an kaishi ne a jerin gwanon motocin dake garin Rashidin dake Yammacin Aleppo.

Kasar Iran da Qatar suka jagoranci kulla yarjejeniyar kwashe fararen hulan daga kauyukan Fouaa da Kefraya wadanda aka yi masu kofar rago.

Babu wani bayani game da wanda ya kai harin.

Mutane sama da dubu biyar ne aka yiwa kofar rago na tsawon shekaru biyu a kauyukan biyu bayaga wasu mutanen 2,200 da za’a kwashe daga yankuna biyu dake hannun ‘yan tawaye Madaya da Zabadani.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.