Isa ga babban shafi
Mu Zagaya Duniya

An kai wa Faransa hari gabanin zaben shugaban kasa

Sauti 20:46
An jibge dubban jami'an tsaro don bada kariya a yayin gudanar da zaben Faransa
An jibge dubban jami'an tsaro don bada kariya a yayin gudanar da zaben Faransa REUTERS/Benoit Tessier
Da: Abdurrahman Gambo Ahmad

Shirin mu zagaya duniya na wannan makon tare da Salissou Hamissou ya tattauna ne kan muhimman abubuwan da suka wakana a fadin duniya da suka hada da takun saka tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa kan gwajin makamin Nukiliya da kuma harin ta'addancin da aka kai a wata kasaitacciyar unguwar Champs Elysee da ke birnin Paris, in da wani jami'in 'yan sanda ya rasa ransa. An bayyana Karim Cheurfi mai shekaru 39 a matsayin wanda ya kai harin a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zagayen farko na zaben shugabncin kasar a ranar Lahadi. Kazalika shirin ya tattauna kan matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na dakatar da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da ake zargi da halasta kudaden haramun.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.