Afrika ta Kudu

Kotu ta dakatar da yarjejeniyar Afrika ta Kudu da kasashen duniya

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma Reuters/Rogan Ward

Kotun Afrika Ta Kudu ta dakatar da yarjejeniyar da gwamnatin kasar ta cimma da wasu manyan kasashen duniya don samar da sabbin tashoshin makamashin wutar lantarki a kasar. Ana kallon hukuncin Kotun a matsayin nasara ga kungiyoyi masu zaman kansu da ke adawa da shirin. 

Talla

Babbar Kotun da ke birnin Cape Town ta ce, gwamnatin kasar ta gaza tuntubar Jama’a gabanin cimma yarjejeniyar da kasashen Rasha da Amurka da Koriya ta Kudu don gina manyan injinan sarrafa makamashin samar da wutar lantarki.

Kungiyoyin gwagwarmayar kare muhalli karkashin jagorancin Earthlife Africa ne suka kalubalanci shirin a kotu, bayan sun ce, gwamnatin kasar ba ta yi cikakken nazari ba kan kudaden da shirin zai lakume  da kuma tasirinsa ga muhalli.

Sai dai hukuncin na Kotun Cape Town bai shafi yarjejeniyar da Afrika Ta Kudu ta cimma da kasashen China da Faransa ba.

A cikin tsawon shekaru, Afrika Ta Kudu na ta kokarin samar da wadatacciyar wutar lantarki a kasar, abin da zai kawo karshen rashin wuta da ke haifar da koma-baya wajen habbakar tattalin arzikinta.
 

Gwamnatin Afrika Ta Kudu ta ce, sabbin injinan makamashin za su samar da karin Megawat dubu 9 da 600 na wutar lantarki.

Kazalika ana saran shirin zai lakume Rand tiriliyan daya, wanda ya yi daidai da Dalar Amurka biliyan 73.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.