Libya

Jami'an Tsaron Gaban Tekun Libya sun Kama Jiragen Ruwa biyu da Man Fetur na Sata

Wani jirgin ruwa a gaban tekun kasar Libya
Wani jirgin ruwa a gaban tekun kasar Libya rfi

Jami'an tsaro a kasar Libya sun kama wasu manyan jiragen ruwa biyu shake da danyen man fetur na sata da matuka jiragen ruwan bayan anyi ta musayar harbe-harbe da su.

Talla

Man fetur ya kasance abinda kasar Libya ke dogaro dashi sosai a matsayin abinda take samun kudaden shiga.

Janar Ayoub Qassem dake jagorantar Jami'an tsaron gaban tekun Libya ya fadi cewa cikin dare ranar Alhamis suka gano jiragen ruwan, daya da tutar kasar Ukraine daya kuma da tutar kasar Congo.

A cewar Jami’in barayin man na da manyan makamai a hannunsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.