Duniya

Kasashen da aikin Jarida ya fi hatsari a Duniya

Jaridun Faransa
Jaridun Faransa REUTERS/Regis Duvignau

Yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar kare hakkin ‘Yan Jaridu ta Duniya, inda masana da ma’aikata ke nazari irin ci gaban da aka samu da kuma akasin haka.

Talla

Kungiyar da ke kare hakkokin 'Yan Jaridu ta bayyana kasar Mexico a matsayin mafi hadari ga ‘Yan Jaridu, ganin yadda aka kashe sama da 50 a cikin shekaru 7.

Bincike ya nuna cewar Gwamnatoci da kungiyoyin 'Yan Siyasa da kuma 'Yan ta’adda ke kai hari ko dirar mikiya kan 'Yan Jaridun dan hana fadawa mutane gaskiya.

Kungiyar ta bayyana wasu kasashen Afirka da aikin Jarida ke fuskantar hadari da suka hada da Masar da Tunisia da Tanzania da Kamaru da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da kuma Burundi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.