Amurka

Majalisar dokokin Amurka ta soke tsarin kiyon lafiya na Obamacare

Shugaban masu rinjaye na Repablican, Paul Ryan a tsakkiya kafin kada kuri'ar soke shirin na Obamacare , 4 meyu 2017.
Shugaban masu rinjaye na Repablican, Paul Ryan a tsakkiya kafin kada kuri'ar soke shirin na Obamacare , 4 meyu 2017. ©REUTERS/Kevin Lamarque

Majalisar wakilan Amruka da keda rinjayen yan Republican ta amince da kudirin soke shirin inshorar kiyon lafiya da gwamnatin shugaba Barack Obama ta samar, al’amarin da ke nuna soma sauye sauyen da shugaba Donald Trump ke son aiwatarwa akan manufofin gwamnatin da ta gabace shi.

Talla

Majalisar dokoki ta amince da kudirin soke dokar insharar ne a cikin gaggawa, bayan da wakilai 217 suka kada kuri’ar amincewa da manufar, a kan kuri’un wakilai 213, daukacin su kuma yan Democrat da wasu yan tsirari da Republican wadanda suka nuna rashin amincewarsu da soke shirin.

Wannan dai na nuna cewa, shugaba Trump ya share rashin nasarar da ya cimma a ranar 24 ga watan maris din da ya gabata a lokacin karatun farko, sakamakon rashin samun jituwa tsakanin yan majalisar ta Rep masu rinjaye, duk kuwa da matsin lamba da suka fuskata, inda aka tilastawa repubilican da ta jaye kudirin na farko awa guda kafin soma zaben

Shugaban masu rinjaye na Repablican a majalisar dokokin Paul Ryan, ya ce amincewa da dokar na nini, da cika alkawarin da suka daukarwa amerikawa ne, tare da danganta tsohon shirin na Obamacare, da aka amince da shi a 2010, da zama batan bashira.

A lokacin da yake bayyana godiya ga shugaba Donald Trump kan rawar da ya taka wajen cimma wannan nasara Paul Ryan ya ce sun jima suna jiran wannan rana tsawon shekaru da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.