Libya

Ana fargabar mutuwar bakin-haure 200 a teku

Ana fargabar mutuwar bakin-haure 200 a tekun Baharu-rum
Ana fargabar mutuwar bakin-haure 200 a tekun Baharu-rum REUTERS/Darrin Zammit Lupi/File Photo

Sama da bakin-haure 200 ake fargabar mutuwarsu a tekun Baharu-rum sakamakon nutsewar jirgin da ke dauke da su a kokarinsu na tsallakawa zuwa Turai.

Talla

Mutane akalla dubu 7 da 500 aka ceto a tekun daga ranar Alhamis zuwa wanann lokaci, kamar yadda masu kula da gabar ruwan Italiya da Libya suka shaida.

Wasu mutane da aka ceto sun shaida wa hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya cewa, daruruwa sun fada ruwa a lokacin da kananan jiragen roba da ke dauke da su suka fara sacewa.

Ko a ranar Asabar da ta gabata, an ceto gawarwaki uku daga cikin mutane 60 da suka nutse a tekun kuma jirgin ya bar gabar tekun Libya dauke da mutane 120.

Ana dai ci gaba da samun alkaluma masu karo da juna kan ainihin wadanda suka mutu saboda sabbin bayanai da ake samu daga wadanda suka tsira da kyar.

Rayuwar mata da maza da jarirai na ci gaba da salwanta duk da kokarin da hukumomi ke cewa suna yi wajen ganin an dakile kwararar bakin da ke mutuwa a Teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.