Isa ga babban shafi
Vatican

Fafaroma zai jagoranci gangamin mabiya Katolika a Fatima

Mabiya Darikar Katolika na ibada a Fatima kasar Portugal duk shekara
Mabiya Darikar Katolika na ibada a Fatima kasar Portugal duk shekara REUTERS
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 2

Shugaban darikar Katolika Fafaroma Francis zai jagoranci gangamin mabiya da ke ziyarar Fatima a kasar Portugal a yau Juma’a domin cika shekaru 100 da abin da suke kira bayyanar isharar Maryama mai tsarki mahaifiyar Annabi Isah (AS) da suke bautawa.

Talla

Dubban mabiya katolika ne ke zuwa duk shekara garin Fatima a Portugal domin ziyara inda aka ce Maryama mai tsarki ta bayyana tare da bada ishara ga wasu makiyaya guda uku.

A garin Fatima a Portugal aka bayyana cewa Maryama mai tsarki ta bayyana ga wasu yara guda uku makiyaya da ta ba ishara tsakanin watan Mayu zuwa Oktoban 1917.

Akan haka ne garin na Fatima ya koma wajen ibada inda dubban mutane mabiya darikar katolika ke tururuwa duk shekara.

Mabiya kusan miliyan 8 za su ziyarci fatima a bana, inda Portugal ta dauki matakan tsaro saboda barazanar harin ta’addanci a Turai.

Wasu mabiyan kan yi tafiya mai nisa a kasa a matsayin bauta ga Maryama mai tsarki.

Fafaroma Francis zai jagoranci gangamin mabiyan a yau Juma’a zuwa gobe Asabar, kuma shi ne fafaroma na hudu ya kai ziyara Fatima.

Mabiya darikar katolika sun yi Imani da cewa Maryama mai tsarki ta ba makiyaya sako guda uku da suka kunshi hasashen aukuwar yakin duniya na biyu, da kuma sakon da sai a shekarar 2000 fadar Vatican ta sanar kan yunkurin kisan fafaroma John Paul na biyu a ranar 13 ga Mayun 1981.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.