Colombia

Ayarin Farko na 'Yan Tawayen FARC da ke kasar Colombia sun mika makamai

Ayarin mayakan 'yan tawayen FARCcikin wani hoto ba da dadewa ba.
Ayarin mayakan 'yan tawayen FARCcikin wani hoto ba da dadewa ba. LUIS ROBAYO / AFP

A kasar Colombia, tarin wasu ‘yan tawayen kungiyar FARC sun kammala tattara makaman da ke hannun su karon farko karkashin wata yarjejeniya da aka kulla bisa jagorancin masu sa idanu daga Majalisar Dinkin Duniya.

Talla

Wata sanarwa daga Majalisar Dinkin Duniya na cewa ‘yan tawayen su 12 sun kasance na farko da suka mika makamansu kuma aka basu takardun shaida da zai basu damar shiga sauran jama'a don gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Tun a bara ne dai aka tsara ‘yan tawayen za su mika makamansu ga Gwamnati, karkashin sa idanun jami'an Majalisar Dinkin Duniya, domin kawo karshen rashin zaman lafiya na tsawon shekaru 53 da ka samu a Colombia.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.