Turai-Afrika

An yiwa Kasashe 99 kutsen bayanan sirri

An yiwa Kasashe 99 kutsen bayanan sirri
An yiwa Kasashe 99 kutsen bayanan sirri REUTERS/John Adkisson

Kamfanin samar da tsaron bayanan shafin intanet mai suna Avast ya sanar da gano sama da kutsen bayanan da aka adana a shafukan Intanet sama da dubu 75 a kasashen duniya 99.

Talla

Kamfanin Avast ya ce kutsen da ya shafi manyan ofisoshin gwamnatoci, asibitoci, da kuma kamfanoni, shi ne mafi muni da aka taba gani tun bayan fara amfani da shafin intanet.

Kutsen dai ya fi shafar kasashen Rasha, Ukraine da kuma Taiwan, koda yake wasu manyan asibitoci a kasashen Birtaniya da China sun bayyana cewa, suma kutsen ya shafe su.

Kutsen ya na illa ga na’ura mai kwakwalwa ta hanyar kulle dukkanin wasu muhimman bayanai da ke kanta, tare da bukatar duk wanda ya mallake ta ya biya adaddin wasu kudade cikin awanni 6 kafin ya samu damar bude su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.