Lafiya

Kasashen Afrika ne karshe a fannin ci gaban kiwon lafiya a duniya

Switzerland ce kan gaba a ci gaban kiwon lafiya a duniya
Switzerland ce kan gaba a ci gaban kiwon lafiya a duniya Getty image/ David Sacks

A wani bincike da aka wallafa kan ci gaban fannin kiwon lafiya a kasashen duniya, ya nuna kasashen Afrika da ke kudu da sahara ne na karshe ga ci gaban kiwon lafiya a duniya. Rahoton kuma ya nuna Amurka da Faransa da Birtaniya ba su cikin jerin kasashe 10 na sahun farko.

Talla

An gudanar da binciken ne na The Lancet kan ci gaban kiwon lafiya a kasashe 195 da aka kaddamar a ranar Juma’a.

Binciken ya nuna daga cikin kasashen duniya 195, Kasar Switzerland ce kan gaba a duniya sai Iceland da Sweden da Norway da Andorra da Australia da Finland da Netherlands da Spain da suka kasance a jerin kasashe 10 na farko.

Haka ya nuna manyan kasashen duniya kamar Amurka da Faransa da Birtaniya ba sa cikin kasashen 10 da ke sahun gaba.

Amurka ta kasance kasa ta 35, Faransa ta 15, Australia da Japan na 11, yayin da Birtaniya ke matsayi na 30.

Baya ga kasashen Haiti da Yemen da Afghanistan, kasashen Afrika ne sauran kasashe 30 na karshe a rahoton. Kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ce rahoton ya bayyana mafi muni.

An gudanar binciken ne ta la’akari da inganci da kusancin kiwon lafiya ga jama’a tare da auna yawan mutanen da ke mutuwa a cututtuka sama da 30 da za a iya maganinsu.

An gudanar da binciken ne tsakanin 1990 zuwa 2015, inda rahoton ya nuna kasashe kamar China da Turkiya da Koriya ta kudu sun samu ci gaba a fannin kiwon lafiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.