FRANCE-INDIA

Shugaban Faransa ya karbi bakuncin Firaministan India

Firaministan India Minister Narendra Modi a lokacin da shugaban Faransa  Emmanuel Macron ke tarbansa yau Asabar
Firaministan India Minister Narendra Modi a lokacin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ke tarbansa yau Asabar REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karbi bakuncin Firaministan kasar India Narendra Modi a birnin Paris, inda suka tattauna harkokin da suka shafi ciniki da kasuwanci da tsaro na tsawon sao’i biyu.

Talla

Firaministan  India Narendra Modi ya yi amfani da damar wajen jaddada cewa India na cikin yarjejeniyar da aka kulla dangane da batun magance dumamar yanayi, wanda ake kira 'Paris deal'.

Ya tabo wannan batu ne yau Asabar  kwanaki biyu bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da ficewar Amurka daga dukkan yarjejeniyar da aka kulla gameda rage dumamar yanayi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.