Amurka

Kotu ta sake yin watsi da dokar Trump kan baki

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlos Barria

Wata Kotun daukaka kara ta Amurka ta ki amincewa da bukatar shugaban kasar Donald Trump na janye dakatarwar da wata kotu ta yi wa umrninsa na hana baki shiga Amurka daga wasu kasashen Musulmi 6.

Talla

Alkalan kotun sun ce, shugaban kasar ya gaza wajen gabatar mu su da kwararan shaidun da ke nuna cewar, mutanen da ke shiga Amurka daga wadannan kasashen Musulmin 6 na da hatsari ga rayuwar Amurkawa.

Wannan hukuncin na zuwa ne bayan irinsa da wata karamar kotu ta bayar a cikin watan Mayu a Virginia wanda ya yi dai dai da na kotun Maryland.

Kasashen da shugaba Trump ke son haramta mu su shiga Amurka sun hada da Libya da Iran da Somalia da Sudan da Syria da Yemen.

Gwamnatin Trump ta ce, akwai bukatar daukan wannan matakin don hana ‘yan ta’adda samun damar shiga Amurka.

Sai dai shirin na Trump ya gamu da suka, in da masharhanta suka bayyana haka tamkar nuna wariya ga wani bangare tare da fadin cewa, ya kuma saba wa dokar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.