MDD

India za ta zarta China da yawan Jama’a a 2050

China ta zarce India da yawan jama'a a.
China ta zarce India da yawan jama'a a.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen duniya zai tashi daga bilyan 7 da milyan 600 zuwa bilyan 9 da milyan 800 a shekara ta 2050, kuma Najeriya za ta kasance kasa ta uku mafi yawan jama’a a duniya a lokacin.

Talla

Hasashen ya ce yawan jama’ar kasar India zai zarta na China kafin shekara ta 2050, wanda zai bai wa India damar kasancewa jagora ta fannin yawan jama’a a duniya.

India ta biyu da yawan jama’a a yanzu za ta zarce China da yawan jama’a a 2024, a cewar rahoton.

Rahoton wanda sashen Tattalin Arziki da Kyautata Rayuwar Al’umma na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya ce Najeriya, kasar da ta fi kowace yawan jama’a a nahiyar Afirka, za ta sha gaban Amurka domin kasancewa kasa ta uku mafi yawan al’umma a duniya kafin shekara 2050.

A kowace shekara ta Allah ana samun karuwar mutane sama da milyan 80 a sassan duniya, kuma idan aka ci gaba da tafiya a haka adadin mutanen duniya zai kai bilyan 8 da milyan 600 a cikin shekaru 13 masu zuwa, sannan adadin zai kai zuwa bilyan 9 da milyan 800 a shekara ta 2050.

Rahoton ya ce a nahiyar Afirka akwai wasu kasashe guda 26 da yawan jama’arsu zai rubanya har sau biyu kafin shekara ta 2050 matukar aka ci da samun haihuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.