Colombia

Nakiya ta Kashe Mutane 8 Wajen Hakar Ma'adinai a Colombia

Tsakiyar birnin Bogota
Tsakiyar birnin Bogota rfi

A kasar Colombia nakiya da aka dasa a wurin hakar ma’adinai ta hallaka mutane takwas yayinda wasu mutanen biyar suka bace.

Talla

Majiyoyin samun labarai a Bogota na cewa an sami hadarin ne a garin Cucunuba dake jihar Cundinamarca mai tazaran kilomita 90 daga birnin Bogota.

Hukumomi a yankin na cewa mutun daya na nan ya sami raunuka.

Shugaban kasar ta Colombia wanda yanzu haka yake karkare rangadin da ya kawo Faransa ya aike da sakon ta'aziya ga dangi da ‘yan uwan mamatan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.