Paris

Boeing da Airbus sun ci kasuwa a baje-kolin jiragen sama a Paris

Bikin baje-kolin jiragen sama ta Bourget, a bana ba ta yi mutane ba a Paris
Bikin baje-kolin jiragen sama ta Bourget, a bana ba ta yi mutane ba a Paris © REUTERS/Pascal Rossignol

Bikin baje kolin-jiragen sama na Bourget, karo na 52 kuma mafi girma a duniya da aka gudanar a birnin Paris na Faransa, ya kawo karshe, tare da samun karuwar masaya jiragen sama da kimanin kashi 13% duk da cewa an samu karancin mahalarta a bikin na bana sakamakon dokar ta-baci da ake amfani da ita a kasar.

Talla

A bikin baje kolin na bana, wanda kamfanonin kera jiragen sama daga sassa daban daban na duniya suka halarta, an yi ciniki da kuma odar jiragen da sauran na’u’rorinsu da ya kai dala bilyan 150, sabanin shekara ta 2015 inda aka yi cinikin dala bilyan 130.

Bajen kolin wanda ake gudanarwa a kowadanne shekaru biyu, a bana manyan kamfanonin kera jirage a duniya Boeing da kuma Airbus kawai, sun yi cinikin dala bilyan 114, inda Boeing na Amurka ya yi cinikin dala bilyan 74, yayin da Airbus wanda mallakin wasu kasashen yankin Turai ne ya yi ciniki dala bilyan 39.

Akwai wasu kamfanoni da suka shahara ta fannin kera na’urorin jiragen sama da suka hada da CFM International, da General Electric da kuma Safran, da suka kulla ciniki na milyoyin kudade a baje-kolin da aka kammala.

A bana an samu mutane dubu 140 ne da suka ziyarci kasuwar baje-kolin, abin da ya gaza na shekaru biyu da suka gabata da kimanin 6%, kuma ana danganta hakan da yanayin tsaro da kuma dokar ta-baci da aka kafa a kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.